Sultan Abdul Hameed Khan na II (21st September 1842 – 10 February 1918) Khan ɗaya ne daga Sarakuna ƙarshe-ƙarshe na Daular Usmaniyya da akayi a ƙasar Turkiyya, yayi khalifanci tsakanin 1876 zuwa 1909. Abin sha’awa wannan Sarki ƙwararren kafinta ne har yanzu akwai wasu kayan furnitures da ya ƙera da hannunsa a wasu manyan fadodi tarihi a Istanbul na Turkiya. Ta fuskar Addini da Sufanci a zamo mai tsananin son Annabi Sallallahu alaihi Wasallama da kishin Musulunci kuma sufi ɗan Ɗarikar Shazaliyya. Akwai ƙasidarsa ya tawassuli da Annabinsaw da aka rubuta a jikin raudar Annbai saw yana cewa a farkon ta: يَا سيِّدي يا رســولَ الله خُذْ بيدِي ما لي سِواكَ ولا أَلْـــوي على أحد فــأنتَ نورُ الهدى فــي كلِّ كَائِنَــةٍ وأنتَ سرُّ الندى يا خيـــرَ معتمــدِ و أنتَ حقًــا غياثُ الخلقِ أَجْمَعِهِمْ وأنتَ هادي الورى للهِ ذي السّـــدَدِ Ya fuskanci takurawa da makircin Turawan yamma, da ƙokarin kashe shi saboda yadda ya hana a kawo Yahudawa cikin ƙasar Palastinu da hana yaduwar daulolin Europe. Makircin yakai har sai da akai amfani da yan bokon ƙasar sukai juyin juya halin da ya kauda khalifancinsa karshe ma aka soke Khalifa aka kafa daular Turkiyya ta Demokradiyya ƙarkashin Mustapha Kamal Atatürk. A wanna bidiyon daga cikin wasan kwaikwayon rayuwarsa ne, wani bawan Allah yayi mafarki da Annabinsaw ya aiko shi wajen Sultan Abdul Hameed yana tuna masa cewa jiya ya manta salarin da yake masa da daddare.
Hide player controls
Hide resume playing